Rababben Birni (2): Addini Ya Raba Mazauna Jos, Kwallon Kafa Tana Hadasu
A kokarin da Jos ke yi wajen farfadowa daga rikicin addini da na kabilanci da ya kaureta wajen shekara 20, wasan kwallon kafa ne yake kokarin hada kan mutane. Wannan kaso na biyu ne a jerin labaran da Nathaniel Bievan ya rubuta, Aliyu Dahiru ya fassara.
Matasa ne yan kwallon kafa da ke tsakanin shekara 18 zuwa 25 da suka fito daga sassa daban-daban na birnin Jos, wani gari da ya yi fama da rikice-rikice a Arewa ta tsakiyar Nigeria. Sun hadu ne a ranar Lahadin bikin Easter, 14 ga Afrilu, 2021, kuma ba shi ne karo na farko ko na karshe da suka taba haduwa don wasan ba.
Kungiyar âFace of Peace Globalâ ce ta tattarasu. An rarrabasu zuwa kungiyoyin âReconciliationâ (Sulhu), âPeaceâ (Zaman Lafiya), âLoveâ (Soyayya), âHumanityâ (Mutuntaka), da âForgivenessâ (Yafiya). An cakuda tsakanin matasan musulmi da na kirista domin buga wasan da zai kara alakar da addinai ko kabilu suka tarwatsa.
Amma ta yaya aka fara hakan?
Kirkirarrun Iyakoki
Hatsaniyar da ta fara a 2001 a Jos ta ci gaba da hargitsa garin akai-akai har zuwa 2019. Lokacin da rikicin yan asali da baki ya kara tsamari, sai Kiristoci (wadanda mafi yawa yan kabilar Berom, Afizere da Anguta ne) da Musulmi (mafi yawa yan kabilar Hausa da Fulani) suka canja guraren zama zuwa inda suke ganin yafi musu kwanciyar hankali; wato dai guraren da masu bin addinansu suka fi yawa.
Wannan shi ne dalilin da ya sanya Salis Muhammad Abdulsalam, wanda ya kirkiri kungiyar âFace of Peaceâ, ya shirya wasannin âMusic Plus Footballâ.
Gurin da Abdulsalam yake aikinsa zai tabbatar maka da suna samun nasarar abin da suke son su aikata. A allon bango za ka tarar da hotunan wasannin da aka yi a baya da suke nuna maka cewa lamarin ya yi nisa.
Sai dai abin takaici kuma shi ne maâaikatansa na kashe kudin mota da yawa kafin su tsallako gurin aikinsu saboda wasu kirkirarrun iyakoki da suka raba garin zuwa biyu.
Cikin kaduwa da girgiza, Abdulsalam ya fadawa HumAngle cewa, âyanayin rikicin Jos yana sanyawa a sha wahalar yadda za a iya kawo zaman lafiya da zai amfani.â
Ya bayyana cewa, âmun samu hare-haren taâaddanci, na addini, na kabilanci, na manoma da makiyaya. Amma yanzu matsalar da muke yaka ita ce ta rabuwar kan mutane ta yadda suke zaune kawai da wadanda mabiya addininsu ne. Idan ba ka san Jos yadda ya kamata ba, za ka iya tsallakawa wani bangaren ka aikata abin da zai janyo a yi maka abin da bai kamata ba.â
Duk da wadannan kirkirarrun iyakoki basu da wata alama, ya bayyana cewa suna nan a zuciyar wadanda suke riko da su.
Wannan shi ne abin da kungiyar mai zaman kanta ta shigo ciki don ta gyara, kokarin da a cewarsa shi ne zai hada kan makotan guda biyu. Amma lamarin na da ban wahala saboda yadda mutane suka saba da abin da bai kamata ba.
âMutane suna jin kwanciyar hankali idan suka ga wani irinsu ne yake makotaka da su. Hadarin shi ne a irin haka ake boye wasu laifuka kamar na kisa, cin zarafin kananun yara, da sauran abubuwan da ake rufewa saboda haka,â Abdulsalam ya bayyana. âDon kawai mai laifi irinka ne.â
Wasan Kwallon Kafa na âMusic Plusâ
Lokacin da Abdulsalam ya bayyana damuwarsa kan wadannan kirkirarrun iyakoki da mazauna Jos suka kirkira, kokarinsa na ya magance wannan matsala ya fara ne a rikicin 2001 da ta gwamutsa kabilu mabanbanta musamman na Hausa, Fulani, Berom, Afizere da Anaguta. Wannan shi ya rikide ya zama babban rikicin addini.
Kocinan kungiyoyin kwallon kafa kamar Bature Magaji Muhammed na Team Unity da kuma Victor Chasu na kungiyar Team Love suka fita suka fara aiki. Suka dinga zagayawa daga wannan gari zuwa wancan domin harhada yan wasan da za su shiga shirin Music Plus Football da ya yi shirin sabunta alakar makotan da suka watse.
Chasu, wanda kirista ne, ya zagaya makota kamar su Duala, Bulbula, Filin Ball da Kuma Congo-Russia domin ya tattara yan wasansa – so yake ya hada takwas daga cikinsu musulmi haka ragowar takwas din kirista. Da ya gama tattarasu sai ya ce musu su fara shiri.
âNa gaya musu cewa akwai bukatar mu hadu ma samar da canji a wannan alâumma, mu hadu akan abin da ya hada duka garuruwan,â ya fadawa HumAngle.
Daga nan kuma sai ya gayyacesu gidansa inda ya fara kokarin gudanar da abubuwa. Aka huta, aka yi wasa, aka ci abinci; ta haka yan wasan suka dinga sauraran duk abin da kocin nasu ya gaya musu. Bayan wadannan ranaku, Chasu ya tabbatar da ya ziyarci kowane dan wasa a gidansu. Ta haka aka haifar da Team Love.
Tamkar abokin aikinsa, Mubammed koci ne musulmi da ya tattara yan wasansa cikin gaggawa a shekarar 2020. âYanzu tare muke yin komai,â ya fada. âWasu sun fito daga Rikkos, Nasarawa da kuma Dutse Uku.â
Da farko lamarin bai yi armashi ba, Muhammad ya bayyana. Yan wasan sun fara babu fahimtar juna kamar yan uwa. Daga baya aka samu ci gaba.
Dan wasa mai tsaron gida a kungiyar Team Love, Pankeys Isa mai shekara 20, ya bayyana tsoron da ya fara ji da farko lokacin da yake tunanin yan wasan kungiyarsa musulmi ba za su fahimceshi ba. Daga baya ya fahimci cewar yana da abubuwa iri daya da mafi yawan yan kungiyar tasa.
âYanzu bamu da wannan tunanin mara kyau da muka dinga yiwa junanmu a baya,â ya bayyana. Yanzu yana shiga Filin Ball, Dutse Uku da Unguwar Rogo; unguwannin da a baya sun fi karfin kirista kamarsa.
Sadiq Jayjay mai shekara 18, a nasa bangaren, yana tuno lokacin da suke haduwa da abokansa kiristoci. Dalilin haka, damar na zuwa ya yi sauri ya shigeta. Musamman ma saboda a baya yana buga kwallon kafa tare da abokansa na wani addinin kafin rikicin ya balle.
Ba kamar ragowar da a da can baya suke rasa abokan muâamala idan rikici ya balle ba, shi Jayjay ya koma amfani da kafafan sada zumunta. âWannan ita ce kadai hanyar da zamu bi tun da babu wani zabin,â ya bayyana. Yanzu yana zaune a Congo inda aka samu ci gaba har kiristoci da musulmi ke makotaka kuma suke muâamala da juna.
âDa akwai wani dadi da za ka ji idan kana zagayawa duk inda kake so a garin da ka yi rayuwarka shekaru da yawa,â haka Sadiq Saleh mai shekara 18 yake ji bayan ya yi nasarar cire wadannan kirkirarrun iyakokin da a da suka samu gurin zama a zuciyarsa. âLokacin rikici ina cikin damuwa,â ya fada. âAmma yanzu ina shiga duk inda nake so maimakon na makale a Nassarawa inda nake zaune da yake cike da musulmi.â
Umar Musa Yunusa mai shekara 25, yanzu haka yana alfahari da kasancewarsa abokin kiristoci da yawa. Guraren da a baya ba a iya zuwa kamar Unguwar Rukuba ko Tina da ke Nasaarawa, a yanzu shi a bude suke a gurinsa.
Amma ba kowa ne yake cin ribar wannan kokarin hadin kan da Jayjay ko Isa ke amfana ba. Mazauna Jos kamar Angela Plang da ta zauna baki dayan rayuwarta a cikin birni, da Aku Michael Joseph, suna jin tsoron shiga inda musulmi suke da yawa.
âKwanan nan na wuce ta hanyar Bauchi. Ban tsaya na saka kafata a gurin ba tun dadewa,â Joseph ya fadawa HumAngle. âHar yanzu a tsorace nake saboda abin da ya faru. Ina jin tsoron kada a maimaita.â
Amma Joseph wanda ya dauki hanyar Bauchi da Unguwar Rogo da suke arewacin Jos guraren da ba za a iya zuwa ba, duk da haka ya bayyana cewa an samu ci gaba a alakar da take tsakanin kirista da musulmi. âIdan ana rigima da ana tsayar da motoci a binciki na ciki, amma yanzu an dena,â ya bayyana.
Wani mazaunin hanyar Bauchi, Umar Sadiq Sabo, sun gudo daga Rusau da take cike da kiristoci bayan rikicin 2008. Daga baya suka koma, amma a 2010 aka sake sabuwar rigimar da ta janyo suka rasa gidansu har suka koma inda suke yanzu.
A wancan lokaci, Sabo yana kula sosai a yanayin motsinsa kuma yana kokarin kin shiga guraren da ya san babu Musulmi da yawa kamarsa irin su Gada Biyu, Unguwar Rukuba da sauran makota. âAmma yanzu ina yawo ko ina,â ya fada.
Wani tsarin na shirin Music Plus Football shi ne a shiga a buga wasa a bangare da yawa na Jos, musamman guraren da suka fi daukan rikici. Ta haka zai janyo garuruwan su ji dadin wasannin kuma su watsar da banbance banbancensu.
Da tsarin shi ne a yi wasannin tsakanin unguwanni, to amma kungiyar Face of Peace Initiative bata son yan wasan su wakilci inda suka fito. âKuma ma ai wasanni ne ba gasa ba,â inji Abdulsalam. âWannan an yi ne don a karfafi alakar yan wasan ta fuskar addinai.â
Lokacin da Sabo ya halarci daya daga cikin wasannin da aka fara da Face of Peace ta shirya, ya lura da cewa ana habaka yadda garin zai koma kamar yadda yake a baya – inda za a samu mutane daga mabanbanta addinai da kabilu da suka fito daga sassan kasar nan su zauna tare cikin zaman lafiya.
âWani yunkuri ne da ya kamata saboda yana samar da zaman lafiya,â Sabo ya fadawa HumAngle. âMuna da bukatar hakan tun farko.â
Amma Sabo bai yi tunanin shirin Music Plus Football zai yi nasara ba. Lokacin da ya fara jin irin tunanin ya yi zaton abin ba zai yiwu ba. Babu ta yadda mabiya addinai daban-daban za su iya haduwa su hada kungiya kuma su yi wasa kamar abokai. Amma da ya ga wasan farko sai ya ga abin da bai zata ba – duk sun zama abokan.
Daga can nesa a filin wasa na Barikin Duala, Abdullahi Ismaâil ya kalli yadda Team Peace suka jeru domin su yi nasara kan abokan wasansu.
A lokacin da ana wasan, Ismaâil ya yi wata magana a tsakanin kiristocin da suke kallon wasan. âBan fiye samun irin wannan damar a Gangare, arewacin Jos, inda nake zaune ba,â ya bayyana. âIna nufin wasa ya sa mutane su bar guraren da suke jin suna da tsaro su tawo inda suke tunanin akasin haka zai faru.â
Sannan kuma akwai Sheikh Sheikh wanda shi ma ya kalli wasan da aka yi a Barikin Duala a Afrilu 4, 2021, inda Team Unity suka yi nasara akan Team Peace da ci daya.
âAbin da yafi kayatarwa shine ban iya banbance tsakanin kirista da musulmi ba a filin,â inji Sheikh. âBa Afizere, ba Berom ko Hausa. Kabilarka ba ita ta damemu ba a nan. Kwallon kafa taba da wannan karfin. Tana hada kai. Da za a ci gaba da haka, da rikicin da ake a nan ya zama tarihi.
Click here to read the original report in English: The Polarised City (2): Jos, Divided By Religion, United By Football
Support Our Journalism
There are millions of ordinary people affected by conflict in Africa whose stories are missing in the mainstream media. HumAngle is determined to tell those challenging and under-reported stories, hoping that the people impacted by these conflicts will find the safety and security they deserve.
To ensure that we continue to provide public service coverage, we have a small favour to ask you. We want you to be part of our journalistic endeavour by contributing a token to us.
Your donation will further promote a robust, free, and independent media.
Donate Here